Saturday, 5 August 2017

TARIHIN UMAR M. SHAREEF

Umar Muhammadu Sharif na ɗaya daga mawakan hausa masu zazzaƙar murya da Ubangiji yaima baiwar waƙa, taurarone a harkar kuma ya samu kyaututtuka da dama kan harkar. Ɗan garin Rigasa dake Kaduna ne, haifaffen shekarar 1987 yayi karatun matakin farko da na gaba, wato sakandare duk a garin nasu.

Umar yacce ya kasance ɗan makaranta mai ƙwazo a karatunshi na sakandare kuma yacce shi ya ɗau tafarkinai da hannu biyu-biyu. Abunda ya tsundumashi waƙa shine wani al’amarin da ya faru tsakaninshi da masoyiyayai ta farko, kamar yadda ya bayyanama BBCHausa.

Rubutawa Abdulhadi Followcome
.
Umar m sharif yace Wata rana sadda ina ɗan sarmayi,
akwai wata yarinya wadda nike matuƙar so da ƙauna a unguwarmu, amman kasancewata sabon shiga sai nike jin kumyar tunkararta dan mu zanta.

Ya cigaba, bayan na shaidama abokaina, sai suka shawarcan nai tattaki har gidansu wato naje gidansu na aika tazo. Nayi haka, amman duk lokacinda ta fito dan fuskantan mai kiran, ba wanda take tarardawa a kofar gidan nasu ballantana wanda aka ce yana kiranta. Ni kuma a lokacin ina wani ɓangare ina wasan ɓoyo. Nayi haka kusan so ukku. Sannan, ana nan sai wata ran na ce yau zan yi tsayin daka dan naga abinda zai turema buzu naɗi. Sadda na isa ƙofar gidansu kamar kullum, na aika mata tazo ina kiranta, amman yarinyar taki ta fito, wata matsala sabuwa kuma. Sai na tuno yadda nai wasa da hankalinta na gano ba zata zo ba dai. Yayinda nake nan ina cikin jiran kiran da ba karɓawa, sai hawaye suka kwararo kumatuna, a wannan halin na tsinci kaina ina rera waka. Daga nan nai ta waka har kofar gidan mu. Umar yacce yakan rera waƙa duk lokacinda ya tuno abun. Sannan kuma dama akwai abokin magajinai wanda shima mawaƙine, ya saurari wakarshi wata rana, shi ya bashi shawarori game da waƙa ya kuma taimakamishi wajen haɗa wakatai ta farko.

Umar M Sharif yacce yanada fiye da wakoki 500 inda ya zanyano; Duniya Ce, Nadiya, Madubi, Jinin jikina, Mai atamfa, Bakandamiya da Babbar yarinya a matsayin bakandamiya. Umar M Sharif bayan ya kasance shahararren mawaki, dan wasane kuma mai shirin wasan kwaikwayone a masana’antar Kannywood. Shirin da ya fito ko ya shirya sun haɗa da; Mahaifiyata, Nas, Jinin jikina, Ba zan barki ba, ka so a soka d.s.s

Yayinda aka tambayai iyali, yacce yanada aure da ɗiya kusan biyar. Kwanan baya naga a kafar Instagram, inda ya hauda cewar, yana samun sauki bayan hatsarin da ya samu. DanZubair ɗaya daga masoyanka na maka fatan sauƙi cikin gaggawa daga

No comments:

Post a Comment