Friday, 4 August 2017

TARIHIN NURA M. INUWA

TAKAITACCEN TARIHIN MAWAQI NURA M. INUWA
.
Mu fara da jin takaitaccen tarihinka.
Assalamu alaikum, cikakken sunana shi ne, Nura Musa Inuwa, amma a yanzu an fi sani na da Nura M. Inuwa. An haife ni a Kano, a 1989, kuma na yi makarantar firamare a Masaka Special Primary School, daga nan na yi makarantar sakandare a Gwammaja II. Daga nan ne kuma ban ci gaba da karatu ba saboda wadansu dalilai da suka sha karfina, wanda daga nan na fara harkar waka.
.
Me ya ja hankalinka ka fara waka?
Tun ina karami nake waka, wanda a lokacin ban san me nake yi ba. Wani lokaci ko da wani abu aka yi mini a gida walau na farin ciki ko bakin ciki sai na yi waka a kai. A takaice na fara waka tun ina yaro. A zahirin gaskiya ba ni da tunani na wani dalili da ya sa na fara, sai daga baya na gane cewa zan iya aika sako ta hanyar waka.
.
A kasar Hausa ana daukar mawaka marasa abin yi, inda har ake musu ganin masu bata tarbiyya maimakon gyara ta ko me za ka ce a kan hakan?
.
Hmmm, duk wanda yake waka ba za a ce masa marar aikin yi ba, wani yana da abn yin amma kawai ya fi son ya yi wakar ne, sannan maganar bata tarbiyya kuma ya danganta da irin abin da shi mai wakar ya fito da shi, jama’ a suka ji. Don haka shi mawaki yana da kyau dai ya dinga fadar abin da zai amfani jama’a ba kawai abin da ya ga dama ba, sannan idan mutum daya ya yi abu a waka wanda ana ganin ba mai kyau ba ne, to su kuma masu saurare kada su dauka duka mawaka ne. A’a, shi wanda ya yi wannan abin shi ne, saboda abin da wani yake yi, ba shi wani zai yi ba.
.
Ana yi maka lakabi da ‘Mai Makogwaron Zinari’ ko ta ina ka samo lakabin?
.
Ni kaina na yi mamakin da na ji ana kira na da haka. A zahirin gaskiya masoyana ne suka sa mini sunan.
.
Shekara nawa ka dauka a harkar waka, kuma ya zuwa yanzu ka yi wakoki kamar nawa?
.
Yanzu haka ina da shekara biyar a harkar waka, kuma yanzu ba zan iya cewa ga adadin wakokina ba, amma dai ina jin wakokin da na yi za su kai 100.
.
Ko kana da bakandamiya daga cikin wakokinka, kuma me ya sa ka zabe ta?
.
Gaskiya ba zan zabi bakandamiya ba yanzu, kasancewar wakokin da aka san ni da su suna da yawa, kuma sau da yawa nakan ji a wurin mutane sukan ce wannan waka tafi, amma idan suka sake jin wata sai kuma su ce tafi. Don haka wadda mutane suka fi so ni ma ita na fi so, kafin nan gaba na fitar da bakadamiyata.
.
Ko za ka fada wa masu karatu kadan daga cikin wakokin da ka yi, walau na fina-finai ko na tallace-tallace ko na siyasa da  sauransu?
.
Gaskiya duk a bangaran da ka lissafa babu wanda ban yi waka ba, kamar a fim akwai irin su ‘Rai Dai’ da ‘Aisha Humaira’ da ‘Badi Ba Rai’ da ‘Soyayyar Facebook’ da ‘Sayyada’ da ‘Zurfin Ciki’ da sauransu, amma na siyasa ba za su kirgu  ba.
.
Sau da dama ana rade-radin rubuta maka waka ake yi, shin mene ne gaskiyar maganar?
.
To, a gaskiya ba a rubuta mini waka. Ni nake rubuta wakata da kaina. Sau da yawa wadansu wakokin nawa ba ma rubutawa nake yi ba.
.
Mutane na korafin ba ka yin kundin wakokin bidiyo, kamar sauran takwarorinka mawaka me za ka ce kan hakan?
.
Alhamdu lillah, mutane su yi hakuri, ina kuma sanar musu yanzu haka na gama daukar sabon kundin wakokina, kuma zai fito nan ba da dadewa ba.
.
Ko kana da ubangida a harkar waka, wanda ya yi maka jagora a harkar?
Gaskiya ba ni da ubangida a harkar waka, Allah shi ne Ya iya mini da iyawarSa, amma ba wanda ya koya mini waka ko kuma nake tare da shi matsayin ubangida, sai dai ina girmama Ibrahim Ibrahim domin na dauke shi matsayin yayana ba ubangida ba, kuma idan har shawara zan nema a mawaka shi ne wanda nake ganin zan iya nema a wajensa, kuma na fada matsayinsa ya wuce na ubangida yayana nake daukarsa.
.
Kwanakin baya an kawo maka hari har ya yi sanadiyyar kwanciyarka a asibiti. Me kake gani ya kawo hakan?
.
Ba ni da wani abu da nake tunanin ya ja hakan. Ni dai na dauka kaddara, kuma su wadanda suka yi su suka san dalilin da ya sa suka yi mini, amma na san ban yi wa kowa laifi ba. Na bar wa Allah komai, Shi ne zai yi mini sakayya ranar da suka manta da ita.
.
Ka yi wa masu karatu bayanin yadda al’amarin ya faru?
.
Wani ne ya kira ni ya ce zan yi masa wakar aure, wai matar da zai aura ta ce ni take so na yi mata waka, shi kuma ba mazauni ba ne, don haka ya ce in daure in zo in karbi kudi da na sunayen da za a sanya a wakar, ni kuma sai na je gudun kada ya zarge ni da girman kai, sai na je inda ya fada mini. Daga nan ban san hawa da sauka ba sai na ji saukar sinadarin acid a jikina.
.
Wane buri kake so ka cin mawa a harkar waka?
.
Nagode Allah, ko iya nan na daina waka ba ni da wani buri face abin da Allah Ya nufa, komai na zama Allah ne ya kai ni. Dan haka Shi Ya san matsayin da zai kai ni a gaba.
.
Wacce shawara kake da ita ga ‘yan fim da kuma sauran mawaka?
.
Mu cire hassada a cikin ranmu, yadda za mu samu hadin kan da na kasa zai dinga girmama babba shi kuma babba ya kare mutuncin na kasa. Wannan  ita ce shawarata.
.
Daga karshe, mene ne sakonka ga masoyanka?
.
Ni dai kodayaushe ina so masoyana su sani ba ni da kamarsu, domin da su nake alfahari. Ina mai gode wa Allah da Ya ba ni su kuma ina kaunarsu kamar yadda suke so na, kai fiye da hakan ma. Don haka ina rokon afuwa ga wanda na sabawa ba tare da na sani ba. Dan Allah masoyana ku zamo masu yi mini uzuri a kodayaushe ko da an ce Nura kaza, kada ku dauka, ku gani da kanku sannan ku yarda. A karshe ina yi muku godiya da fatan Allah Ya bar mu tare.

Na kama wakar dambe saboda gadon gidanmu ce - Iliyasu Alhaji Buda

Abubakar Haruna, a Legas

Wakilin Aminiya a Legas ya sami tattaunawa da mawakin ’yan dambe, Iliyasu Alhaji Buda kaya; wanda ake yi wa lakabi da ‘Waziri’ wanda ya kware wajen yi wa ’yan dambe waka a Lgeas. Ga yadda hirar ta kasance:

Jama’a za su so ka gabatar da kanka.
Sunana Iliyasu, sunan mahaifina Alhaji Buda kaya. Yau ina da kimanin shekaru 23 a duniya. A kauyen kaya aka haife ni, a karamar Hukumar Gumi da ke Jihar Zamfara.
.
Ita wannan sana’a ta wakar dambe, shin gadar ta ka yi ko haye?
Gadon wannan sana’a na yi daga wurin mahaifina. Tun ina dan shekara 18 na fara wakar ’yan dambe..
.
Me ya ba ka sha’awa ka tsunduma cikin harkar kida da wakar dambe?
.
Saboda gadon gidanmu ne kuma duk abin da ka gada ka fi kwarewa a cikinsa. Ba ka ji ana cewa dan gado ya fi dan na koya ba?

Akwai wani lakani da kuke amfani da shi wanda ke hana ’yan damben su huce hushinsu a kanku?
.
Akwai lakani da shiri amma uwa-uba akwai girmamawa a tsakaninmu da ’yan damben, ta yadda ba sa tunnin su huce hushinsu a kanmu..
.
Wadanne nasarori za ka iya bayyanawa ka samu tun lokacin da ka fara harkar waka kawo yanzu?
.
Ni babu abin da zan ce sai godiyar Allah domin mun samu nasarori da yawa saboda lokacin muna tare da mahaifinmu, an taba ba shi kyautar mota da kujerar Makka da gida da sauran abubuwan duniya da yawa. Ka ga ai wadannan abaubuwa nasarori ne masu yawa. Kodayake mahaifinmu ya kasance yana kidan dambe da na siyasa amma hakan bai hana shi yi wa ’yan dambe waka ba a kodayaushe.
.
Me ya sa ka yanke shawarar ka zo Legas ka yi wakar dambe a maimakon ka yi Arewa?.
.
Ba don komai ba sai don so da kauna da ’yan damben Legas ke nuna mini a kodayaushe. Kuma ka san an ce garin masoyi ba ya nisa. Ka ga yanzu na shafe shekara biyar ina kida da wakar dambe a Legas tun muna yi a can kasuwar Alaba har muka dawo nan unguwar Akanimodu.
Wadanne matsaloli ne ke damunka tun lokacin da ka fara waka zuwa yanzu?
E, to akwai matsalolin da ba a rasa ba sai dai ina kara godiya ga Allah Madaukakin Sarki da Ya yaye mini matsaloli kuma ina rokonSa ya ci gaba da ba ni tallafi kuma Ya yi mini jagora.
A cikin ’yan dambe, su wa ka fi yi wa waka, bangaren Arewa ko Kudu da kuma Jamusawa?
Ai mu na kowa ne, muna yi wa kowane dan dembe waka amma akwai wadanda suka fi nuna mana so, mu ma sai mu muna musu so ta hanyar yi musu waka fiye da abokanensu.
.
Abdulhadi followcome

No comments:

Post a Comment